15 Oktoba 2014 - 15:08
Habasha : Al'Shabab Na Shirya Kai Sabin Hare-hare A Birnin Adis-Ababa

Offishin jakadancin Amurka a kasar Habasha yayi kururuwar cewa kungiyar al'shabab ta shirya kai sabin hare-hare a wuraren nishadi na jama'a a birnin Adis-ababa na kasar a kwanakin nan

Akan hakan dai offishin jakadancin na Amurka yayi kira ga 'yan kasar sa dasu yi taka sassan su kauracewa yuraren cudayen jama'a musamen a garin Bole inda filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa yake. Babu dai wani wuri takaimaimai da aka bayana shirin kai hare-haren aman sanarwar ta zayano wasu yurare  dakan iyya fuskantar hare-haren kamar unguwar data kunshi gidajen wakilan offisoshin jakadancin kasashen waje dake kasar.